Amurka za ta fadada hari kan IS

Shugaba Obama na Amurka Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Amurka dai ta dade ta na kokarin ganin ta dakile masu tada kayar bayan kungiyar ta IS.

Shugaba Obama ya bayyana karara cewa ya na da karfin ikon da zai iya fadada da farmakin da sojin Amurka ke kaiwa akan masu tada kayar baya a kasashen Syria da Iraqi.

Fadar White House ta bayyana cewar Mr Obama ya yi wannan tsokaci ne a wani taro da suka gudanar a Majalisar dokokin Amurka.

Sai dai kakakin fadar White House yace Shugaba Obama yace zai maraba da goyon baya daga 'yan majalisun domin nunawa duniya cewar Amurka kanta a hade yake a kokarin ta na ganin bayan 'yan ta'adda na kungiyar IS.

Nan gaba ake saran shugaba Obama zai sanar da matakan da zai dauka, a wani jawabi da ake saran zai yiwa al'umar kasar ta kafafen talabijin.

Dennis Ross tsohon jakada amurka a gabas ta tsakiya, ya shiada BBBC cewa ya kamata shugaba Obama ya yi bayani kan yadda kasashen duniya za su yaki IS a jawabin sa.

Inda Yace bai kamata ace Amurka ce kadai ke yaki da ISIL ba, kamata ya yi ace kassahen duniya da shugabannin larabawa da kungiyoyin 'yan Sunni ne suke yakar kungiyar, hakann zai nuna karara cewa ISIL ita ce ta janyowa kan ta zama mujiya a idanun kasashen duniya.