An sake ambaliyar ruwa a Pakistan

Wasu da ambaliyar ruwa ta rutsa da su a Pakistan. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ba wannan ne karon farko da ake samun ambaliyar ruwa a kasar ta Pakistan ba.

An samu karin ambaliyar ruwa a kasar Pakistan,wanda akalla mutane dari biyu da hamsin da biyar suka rasa rayukansu, ya yin da wasu dubbai suka rasa muhallinsu.

A yankin Punjab manya-manyan duwatsun da aka girke domin tare ruwan su ma ambaliyar ta yi awon gaba da su.

Lamarin da ya bawa ruwan damar shiga gonakin kauyuka inda wasu mazauna wajen ke tunanin sun tsira daga ambaliyar ruwan.

A bangare guda kuma daruruwan mutane ne suka kafa tantina a tuddai tare da kayayyakinsu da kuma dabbobinsu a kusa da su.

Yawancin ruwan dai na shigowa ne daga bakin iyakar Pakistan da makociyarta India, inda nan ma aka samu mutuwar mutane da dama da kuma raba wasu da muhallinsu sakamakon ambaliyar ruwa da ruwan saman da aka sheka kamar da bakin kwarya.