BBC za ta yaki masu satar fasaha

Satar fasahar wasu ta Internet Hakkin mallakar hoto THINKSTOCK
Image caption Satar fasahar wasu ta Internet

BBC ta dauki kwakkwaran matsayi a kan masu satar fasaha ta internet a Australia.

Sashen harkokin kasuwanci na BBC mai watsa shire-shire ga kasashen duniya ya ce kamata ya yi kamfanonin sadarwa na internet su kara tashi tsaye wajen magance satar fasaha ta internet.

Da take maida martani ga sake fasalin manufar gwamnatin Australia a kan masu satar fasaha ta internet, ta bayyana cewa kamata ya yi kamfanonin sadarwar na internet su rinka zama cikin shiri na sa ido ga duk wasu alamu na halayyar da ba su yarda da ita ba a tsakanin abokan huddar su.

BBC ta bayyana cewar 'yan kasar ta Australia 13,000 sun yi yunkurin samun fim na Doctor Who ta haramtacciyar hanya.

BBC din ta cigaba da yin abinda masu 'yancin fasahar da dama suka yi a can baya, tana ba da shawarar cewar kamata ya yi kamfanonin internet su sa ido a kan shafukkan da abokan huddar su ke yawan shiga.

Tace, "abinda yakamata ne ga kamfanonin na Internet su gane halayyar abokan huddar su wadda suke sanya alamar tambaya a kan ta, da kuma alamar da ta nuna wani abokin huddar su ya yi wani abinda ya saba ma hakkin fasaha.

Wannan ya hada da amfani da wasu hanyoyin sadarwa masu zaman kansu wadanda za su hadu da hanyoyin sadarwar dake Brittaniya wadanda za su baiwa masu amfani da su damar kallon shire-shiren da iplayer ke nunawa wadanda ba a samun su a Australia.

A shawarar da ta gabatar a rubuce, BBC din ta ce akwai bukatar gaggawa da ake da ita ta daukar mataki ta magance karuwar da ake samu ta satar fasahar mutane.

Tace, ta goyi bayan fafutukar da ake yi ta ilimantar da masu amfani da hanyoyin sadarwa na Internet, to amma ba ta yanke kauna ga daukar matakai masu tsauri ba kamar na rage gudun hanyar samun bayanai ta internet ta masu aikata irin wadannan laifukka ba.

BBC din ta ce ta goyi bayan a hada kai a bullo da wani tsari, wanda masu 'yancin mallakar fasaha da kamfanonin sadarwa na Internet za su dauki alhakin ragewa tare da kawar da satar fasahar mutane ta internet.

Karin bayani