Hafsoshin ECOWAS sun yi taro a Ghana

Taro kan tsaro Hakkin mallakar hoto AFP GettyImages
Image caption Taro kan tsaro

Ranar Alhamis ne manyan Hafsoshin sojin kasashen kungiyar kasuwancin yammacin Africa wato Ecowas ko CEDEAO suka kammala taronsu na yini uku a birnin Accra na Ghana.

Sun yi taron ne kan yadda zasu taimaka wajen shawo kan matsalar cutar nan ta Ebola, da ta addabi wasu kasashen yankin, da kuma matsalar Boko Haram da Nijeriya da makwabtanta ke fuskanta.

Shawarwarin da suka yanke a wajen taron dai sun kunshi hada karfi da musayar bayanai, kan yadda zasu tunkari matsalolin, da kuma suka hada da fashi a cikin teku.