'Mun tsaurara tsaro a Maiduguri'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Boko Haram na kusantar birnin Maiduguri

Rundunar sojojin Nigeria ta ce ta tsaurara tsaro a kewayen birnin Maiduguri na jihar Borno don kare shi daga harin Boko Haram.

Sanarwar sojojin ta biyo bayan gargadin da kungiyar dattawan jihar Borno a arewacin Nigeria ta yi cewar mayakan Boko Haram sun yi wa birnin Maiduguri kawanya.

A cewar dattawan, mummunan bala'i na nan tafe idan har 'yan Boko Haram suka kaddamar da hari a garin Maiduguri kasancewar a yanzu garuruwan da ke kewaye da birnin na karkashin ikon 'yan Boko Haram din.

Sai dai kakakin shalkwatar tsaro ta Nigeria Manjo Janar Chris Olukolade ya ce ikirarin da dattawan Borno suka yi ba shi da tushe, sai ma tayar da hankalin mazauna Maiduguri da ya yi.

Olukolade ya ce:"Mun tsaurara tsaro don kauce wa duk wani hari da zai kawo matsala ga zaman lafiyan da ake da shi a Maiduguri."

Kakakin sojojin ya kuma ce sojoji na ci gaba da kai hare-hare kan 'yan ta'adda a garuruwan Mubi, da Michika, da Bazza, da Gulak, da Gwoza, da Bama, da Gamboru Ngala da kuma sauran kauyuka da Boko Haram ke kai wa hare-hare.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dubban 'yan gudun hijira sun koma Maiduguri

Tun lokacin da 'yan Boko Haram suka tsanananta kai hare-hare a wasu manyan garuruwan jihar Borno, dubun dubatan 'yan gudun hijira ke ta kwarara zuwa cikin Maiduguri domin neman tsira.

Tun daga watan Yuli zuwa yanzu, 'yan Boko Haram sun zafafa kai hare-hare a jihar ta Borno, inda bayanai ke cewar kungiyar ce ke da iko da garuruwan Gwoza da Marte da Bama da Gamborou Ngala da Dikwa da kuma wasu kananan kauyuka a jihar.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Garuruwan da 'yan Boko Haram suka kwace

Rundunar tsaron Nigeria ta jaddada cewar ba za ta bar wa wasu 'yan ta'adda su yi iko da duk wasu yankunan kasar ba.

Bayanai sun nuna cewar 'yan Boko Haram ne ke iko da wasu garuruwa a jihohin Yobe da kuma Adamawa.