Boko Haram:'Muna cin ɗanyar masara da ganye'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mata da kananan yara na cikin mummanan yanayi

Al'ummomin wasu garuruwa a jihohin arewa maso gabashin Nigeria na cikin mummunan hadari sakamakon gumurzu tsakanin mayakan Boko Haram da dakarun kasar.

A yanzu haka wasu mutane sun makale a kan tsaunuka suna cikin yanayi na gaba kura baya sayaki, a yayin da wasu ke cin ganye da danyar masara domin su rayu.

An shafe kwanaki ana fafatawa tsakanin mayakan Boko Haram da kuma sojojin Nigeria a kokarin da dakarun gwamnati ke yi na kwato wasu garuruwa daga hannun 'yan Boko Haram a jihar Adamawa.

Wata mata ta shaida wa BBC cewar akwai yara da dama da suka nemi mafaka a gidanta kuma ba ta san inda iyayensu suke ba.

Wani mutum shi ma ya bayyana cewar mutane bakwai sun mutu a inda ya boye tare da su amma kuma ba a binne su ba.

Gwamnatin Nigeria na shan suka game da yadda take yaki da Boko Haram a yayin da rikicin ke ci gaba da tsananta.