Zamu shiga Sambisa mu ceto 'ya'yan mu

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar Boko Haram ta karbe iko da wasu daga cikin garuruwan jihar Borno.

A Najeriya yayinda 'yan matan Sakandaren nan 'yan Chibok da 'yan Boko Haram suka sace suke haura kwanaki 150 a hannun wadanda sukai garkuwa da su, iyayen 'yan matan sun ce nan zuwa karshen wata zasu fantsama cikin daji domin neman 'ya'yansu matukar gwamnatin Kasar bata kubutar da su ba zuwa lokacin.

Iyayen 'yan matan sunce sun gaji da jiran gawon shanu, kuma suka ce sun gwammace su mutu wajen neman 'ya'yan nasu.

A jiya ne dai kungiyar nan ta Bring Back OurGirls mai matsawa gwamnati Lamba kan 'yan matan ta gudanar da wani gangamin cika kwanaki 150 da sace 'yan matan.

Daya daga cikin iyayen ya ce gwamnatin Najeriya na musu yawo da hankali akan batun 'ya'yan na su, dan haka su yanzu za su dauki matakin kubuto da su ko ta halin yaya.

Baya ga 'yan matan sakandaren Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace watanni 5 da suka gabata, kungiyar ta sace wasu karin mutanen mata da maza.