Taron hafsoshin Sojin Ecowas a Ghana

Shugabannin kasashen ECOWAS
Image caption Shugabannin kasashen ECOWAS

ECOWASManyan Hafsoshin sojojin kasashen kungiyar kasuwancin yammacin Africa watau ECOWAS sun kammala taron yini ukku da suka gudanar a birnin Accra na kasar Ghana.

Manyan jami'an dai sun tattauna ne kan yadda za su taimaka wajen shawo kan matsalar cutar nan ta Ebola da Boko Haram dake addabar wasu cikin kasashen yankin.

Shawarwarin da suka yanke a wajen taron dai sun danganci hada karfi da musayar bayanai kan yadda zasu tunkari matsalalolin da suka hada da fashi a cikin teku.

Hajia Salamatu Huseini Sulemana Kwamishiniyar kula da harakokin tsaro da zaman lafiya da kuma siyasa ta Kungiyar ECOWAS din ta bayyana cewar daya daga cikin shawarwarin da taron ya yanke sun hada da kira ga 'ya'yan kungiyar su taimaka ma juna idan sun nemi taimako.

Karin bayani