Lagos: Mutane da dama sun mutu a coci

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Babatunde Fashola, gwmanan jihar Lagos

Ganin wani Coci a birnin Lagos ya haddasa mutuwar mutane da dama, inda wasu rahotanni ke cewa, mutane da dama sun halaka.

Wasu kafofin yada labaran Nigeria sun ce, mutane da dama sun mutu.

Hukumar bada agajin gaggawa ta Kasa a Najeriya, NEMA, ta ce, ginin wani na Cocin Synagogue Church of All Nations ne a unguwar Ikotun.

Har yanzu dai hukumomi ba su fitar da alkaluman mutanen da suka mutu ba, amma an ce, ana ci gaba da zakulo gawarwaki.

Jagoran cocin dai fitaccen mai wa'azin kirista nan ne, Pastor TB Joshua.