Sojoji sun kama wadanda suka harbi Malala

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Malala Yusufzai

Sojojin Pakistan sun ce kama mutane goma wadanda ake zargi da shiryawa da kuma kai hari a kan yarinyar nan yar makaranta Malala Yusufzai.

Mai magana da yawun rundunar sojin, Manjo Janar Asim Salim Bajwa ya ce an kuma gano makaman da suka yi amfani da su.

A cewarsa, gungun mutanen suna aiki ne bisa umarnin Mullah Fazlullah, shugaban Taliban a Pakistan.

Shekaru biyu da suka wuce ne 'yan bindiga suka tare makaranta dauke da Malala a kan hanya a gundumar Swat da ke Pakistan suka kuma tambayi ina Malala daga nan suka harbe ta dab da dab har sau uku da zummar hallaka ta.

A lokacin tana 'yar shekaru 15 kuma ta shahara bisa dagewa wajen neman hakkin ilimin 'ya'ya mata a Pakistan.