Wani gini ya rufa a cocin TB Joshua a Lagos

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu mata na kuka sakamakon wani bala'i a baya

An soma gudanar da aikin ceto a harabar wani katafaren coci a birnin Lagos sakamakon ruftawar wani gini.

Hukumar agajin gaggawa ta kasa a Nijeriya, NEMA ta ce wani gidan saukar bakin turawa a cikin cocin TB Joshua, Church of All Nations ne ya rufta a yankin Ikotun da ke cikin birnin Lagos.

Kawo yanzu hukumomi ba su yi bayani game da wadanda lamarin ya rutsa dasu ba.

Amma kuma jaridar Punch a Nigeria ta ce mutane kusan 50 sun rasu.

TB Joshua na daga cikin manyan malaman addinin kirista a Nigeria dake da dubban mabiya.

Yana da farin jini saboda ikirarin warkar da marasa lafiya.