Amurka na neman goyon bayan larabawa

Shugaba Obama Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Obama

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry zai kai ziyara kasar Turkiyyya a yau Juma'a, a wani bangare na ziyarar da yake gabas ta tsakiya do min neman goyon bayan gwamnatoci kan yaki da kungiyar masu tada kayar baya da ke son kafa daular musulunci a Iraqi da Syria wato IS.

Kasashen larabawa goma ciki har da Saudiyya sun mince su taimakawa Amurka a yakin da take yi da IS.

Wannan sanarwa dai ta zo ne jim kadan bayan Mr Kerry ya tattauna da wasu daga cikin shugabannin larabawa a birnin Jedda a na Saudiyya.

Karin bayani