Cuba za ta taimaka wajen kawar da Ebola

Masana kiwon lafiya na Cuba Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masana kiwon lafiya na Cuba

A kokarin da Kasashen duniya ke yi na ganin an shawo kan ci gaba da yaduwar cutar Ebola a Afirka ta yamma, kungiyar hadin kan kasashen Afirka ta AU ta gudanar da wani taro a makon da ya gabata a birnin Addis Ababa na kasar Habasha inda kungiyar ta yi kira da babbar murya ga sauran kasashen Afirka da su ba wadannan kasashe uku da cutar tafi kamari taimako don dakatar da yaduwar cutar.

A wannan karo kuma, Kasar Cuba ce ta yi shelar tura ma'aikatan kiwon lafiya fiye da dari da hamsin Afrika ta yamma don su taimaka wajen dakile yaduwar annobar cutar Ebola a Nahiyar.

Likitoci da ma'aikatan kiwon lafiya hade da wasu kwararru kan kawar da yaduwar cututtuka za su je kasar Saliyo inda za su yi aiki na tsawon watanni shidda.

Karin bayani