Masu shigar mata na dambarwa da Facebook

Hakkin mallakar hoto les sterling
Image caption Cherry Sur Bete, ya ce, Facebook ya sa bangaren bayanan kansa na shafin da cewa ya saba ka'ida

Wani gungun masu wasan shigar mata da daudanci sun bukaci Facebook ya bar su su rika amfani da sunayensu na wasa maimakon na gaskiya a shafin.

Ire-iren mazajen su sama da 2,000 ne suka sa hannu a wta takardar korafi ta neman hakan.

Sai dai kuma kamfanin shafin na Facebook, ya gaya wa BBC cewa, ya sa tsarinsa na amfani da sunan gaskiya ne domin kare jama'a da tabbatar da gaskiya.

Su kuma a nasu bangaren masu shigar matan da 'yan daudun sun bukaci sakaya sunayen nasu ne a cewarsu dominsirri da lafiyarsu da kuma zabi.

Korafin wanda Olivia La Garce da ke Seatle, ya fito da shi, na cewa,''duk da cewa suna yen namu ba su ne na yanka ba, amma duk da haka sunaye ne da suka zama jiki a wurinmu.''

''Wadannan sunaye ne da aka san mu da su kuma muke kiran junanmu da su.''

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Facebook ya kafe cewa ya dauki matakin ne domin kare su kansu masu shigar matan

Wani mai wasan shigar matan Cherry Sur Bete, cewa ya yi,'' mun riga mun yi fice da wadannan sunaye a tsakaninmu da kuma masu kallonmu, tilasta mana mu sauya hakan ba abin da zai haifar sai rudani da damuwa.''

Duk da haka masu shafin na Facebook, sun kafe a kan bin dokar sanya sunan gaskiya ga duk wanda zai yi amfani da shafin.

Suka ce akwai wasu hanyoyin da masu wasan za su iya amfani da su don bayyana kansu.