Ana ci gaba da dumi kan ballewar Scotland

Sarauniya Elizabeth Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption ita ma sarauniya Elizabet ba ta son yankin Scotland ya balle daga Burtaniya.

Ana ci gaba da daukar dumi dan gane da kamfe da ake yi,kwanaki kadan gabannin a gudanar da kuri'ar amincewa da yankin Scotland ya ci gaba da zama a Birtaniya ko kuma ya samu yancin sa.

Tsohon mataimakin jagoran jam'iyyar SNP mai goyon bayan yankin Scotland ya balle daga burtaniya, ya gargadi bankuna da cewa za su fuskanci sakamako idan masu rajin ballewa suka samu nasara a kuri'ar da zaa kada a ranar alhamis mai zuwa.

Wasu daga cikin manyan bankuna da ke da shalkwatarsu a yankin sun ce idan Scotland yayi nasarar ballewa daga burtaniya za su maida adireshin ofisoshin su zuwa birnin landan.

Binciken jin ra'ayin jama'a yace sakamakon kuri'ar ka iya kasancewa kan-kan-kan.