Sojin Ukraine sun fatattaki 'yan aware

sojojin Ukraine Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption sojojin Ukraine

Tsawon safiyar ranar Asabar din nan an rika jin karar harbe harben bindiga daga nesa a tsakiyar birnin Donetsk.

A galibin lokutan akan jiwo amo kamar karar harbin atilare, hakan nan kuma an yi amfani da na'urar harba rokoki wadanda aka rika jiwo kararsu cikin dare, wadanda kuma ga alama an harba su ne daga wani wuri da ke kusa da tsakiyar birnin Donetsk.

Mako guda dai kenan dai da aka kaddamar da tsagaita wuta kuma duk da nasarar da aka yi ta musayar wani fursuna, karar harbe harbe na cigaba da wakana a yankuna da dama na Donetsk.

Pira ministan Ukraine Arseniy Yatsenyuk, ya zargi kasar Rasha da kokarin wargaza kasar Ukraine duk da tsagaita wutar da aka yi a baya bayan nan.

Ya shaidawa taron manema labarai a birnin Kiev cewa burin shugaban Rasha Vladimir Putin, ba wai na ya kwace ikon gabashi Ukraine ne kawai ba, har ma da kasar baki daya.

Karin bayani