Gwamnatin Amurka na barazanar cin Yahoo tara

Kamfanin sadarwa na yahoo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kamfanin sadarwa na yahoo

Kamfanin sadarwa na Yahoo ya ce gwamnatin Amurka ta yi barazanar lankamaya masa tara ta zunzurutun kudi dala 250,000 a rana, idan har kamfanin ya gaza mika ma ta bayanai na masu amfani da kamfanin na yahoo a wajen bincike ta intanet.

Kamar yadda bayanan kotu suka nuna hukumar tsaron kasa ta Amurkar NSA ta nemi kamfanin na Yahoo ya kiyaye da sabbin dokokin leken asiri, abinda kamfanin yace ya saba ma tsarin mulkin kasar ta Amurka.

Kamfanin na Yahoo dai ya gaza samun nasara a kotu wajen kalubalantar bukatar gwamnatin.

To, amma an samu cikakkun bayanai a ranar alhamis lokacinda wani alkali na kotun tarayya ya ba da umurnin a bude wasu kayayyaki da suka danganci shari'ar.

Babban Lauyan kamfanin Yahoo Ron Bell ya ce buga wasu hujjojin da aka yi muhimmiyar nasara ce ta bayyana gaskiya.

Yahoo ya ce gwamnatin ta gyara dokar don neman bayanai na mutanen dake amfani da hanyoyin sadarwa na internet, abinda ya janyo kalubalantar yunkurin a gaban Kotu.

Tsohon ma'aikacin hukumar tsaron kasa Edward Snowden ya fallasa shirin a bara.

To, amma bayanan kotun sun nuna cewa kai ruwa ranar da ake yi game da leken asirin tsakanin kamfanonin sadarwa na internet da gwamnatin Amurka ba yau aka fara shi ba, tun shekaru da dama da suka wuce ne kafin Snowden ya fallasa shirin.

Mr Bell ya kara da cewa sabuwar hujjar dangane da shari'ar wadda jaridar Washington post ta fara nunawa ta jaddada yadda muka bi diddigi kowanne mataki don kaulbalantar leken asiri da gwamnatin Amurkar ke neman yi.

Yace, "a wani lokaci ma gwamnatin Amurka ta yi barazanar lankaya mana tarar dola 250,000 a rana idan muka ki kiyayewa da umurnin ta."

Karin bayani