CAR: Sojojin UN za su karbi aiki yau

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sama da shekaru ashirin Jamhuriyar tsakiyar Afrikan ke fama da tashin hankali.

A yau ne dakarun tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya za su maye gurbin na kasashen Afrika a Jamhuriyar tsakiyar Afrika domin tabbatar da tsaro.

Tun daga bara har izuwa yanzu kasar ta yi fama da tashe-tashen hankula masu alaka da kabilanci da addini da kuma rigingimun siyasa.

Hakan ya sa wasu 'yan kasar da dama yin gudun hijira zuwa kasashen irin su Kamaru da kuma Chadi.

A yanzu dai ayarin motoci kusan dari uku da hamsin ne da wasu jiragen Majalisar Dinkin Duniya suka shiga kasar dauke da kayayyaki.

Sojojin tabbatar da zaman lafiyar da za su isa daki-daki za su kai kusan dubu shida kamar yawan na Afrikan.

Karin bayani