Saudia ta ce ba damuwa a kan cutar MERS

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban musulmi na hallara a Saudia domin aikin hajjin bana

Hukumomin lafiya Saudiyya sun ce suna iyakacin kokarinsu don hana yaduwar cutar MERS mai sa zazzabi da mura da hana kodar mutum da hallaka mutane, yayin da Musulmai ke isa kasar don aikin Hajji.

Cutar ta MERS ta hallaka mutane kusan 300 a kasar ta Saudiyya tun bayan bullarta shekaru biyu da suka gabata.

Kuma a kasashen duniya ta kama sama da mutane 800 inda ta hallaka kashi 40 cikin dari daga cikinsu, yawancinsu a Saudi Arabia.

An zargi hukumomin kasar da yin rufa-rufa akan yaduwar cutar da kuma rashin daukar matakan da suka da ce na yaki da ita.

Sai dai sun ce yanzu sun dauki matakan dakile ta musamman a asibitoci inda a nan aka fi kamuwa da ita.

Duk da wannan tabbaci na hukumomin kasar, hukumar lafiya ta duniya ta ce lamarin abin damuwa ne, ta kuma shawarci duk maniyyacin da yake da wata cuta ya tabbatar ya tuntubi likitansa kafin ya je kasar.