Daruruwan 'yan ci-rani sun mutu a teku

'Yan ci-ranin da suka kubuta Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan ci-ranin da suka kubuta

Hukumar da ke kula masu kaura ta kasa da kasa ta ce kusan mutum dari biyar ne suka mutu a wani hadarin kwale-kwale, wanda ya nutse a kusa da Malta, ranar Alhamis din da ta gabata.

An dai ambato wasu Palasdinawa biyu da suka tsira na cewa da nufi masu safarar mutane suka kifar da jirgin.

A bangare guda kuma, Sojojin ruwan kasar Libya sun ce wani jirgin ya kife da wasu 'yan ci-rani daga nahiyar Afirka da mutum kusan dari biyu da hamsin.