Hukuncin kisa a kan sojoji 12 a Nigeria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Kotun Birgediya Janar Chukwuemeka Okonkwo ya ce hukumomin soji ne za su tabbatar da hukuncin karshe

Wata kotun soji ta musamman a Nigeria ta yanke wa wasu sojojin kasar 12 hukuncin kisa ta hanyar bindigewa bayan samunsu da laifin bore da kuma yunkurin kashe kwamandansu.

Kotun ta kuma wanke wasu daga cikin sojojin da aka tuhume su da aikata wadannan laifuka a daren Litinin.

Kotun sojin wadda ta kunshi jami'ai tara ta yi zama ne a Abuja inda ta tuhumi sojojin kan laifuka shida, da suka hada da bore da yunkurin kisan kai da kin biyayya ga umarni da shugaba da kuma kazafi.

Kotun ta samu 12 daga cikin sojoji 18 din da aka gurfanar da aikata laifukan bore da yunkurin kashe kwamandansu manjo janar Ahmadu Muhammad na sabuwar runduna ta bakwai ta kasar da aka kirkiro a Maiduguri, sakamakon fyaki da dakarun kasar ke yi da 'yan Boko Haram.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dubban mata da kananan yara sun rasa muhallinsu

Su dai sojojin an yi musu wannan shari'a ne sakamakon fushi da suka yi kan kashe abokan aikinsu, inda suka dora alhakin kisan akan kwamandan nasu.

'Yan Boko haram sun yi wa tawagar sojojin kwanton bauna a wani wuri a karamar hukumar Kala-balge ta jihar Borno, yayin dawowa daga garin Chibok, ranar 13 ga watan Mayu bayan wata fafatawa da suka kashe 'yan Boko Haram da dama

Rahotannin sun ce sojojin sun dora alhakin ne akan kwamandan saboda umarninsu da cewa lalle-i-lalla sai sun dawo Maiduguri daga inda suka je fafatawar, alhalin kuwa dare ya yi.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Boko Haram sun kwace iko da wasu garuruwa a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa

Sauran sojojin da ke cikin wannan tawaga da 'yan Boko Haram suka yi wa kwanton bauna ne, suka harzuka suka rika jifan sa da duwatsu da kuma auna shi da harsashi sai da ya nemi mafaka a cikin wata motar yaki, kamar yadda rahotanni suka bayyana, lokacin da aka kawo gawarwakin 'yan uwansu bariki.

Dukkanin sojojin da aka yanke wa hukuncin su 12 sun musanta aikata laifukan.