Taron Paris ya amince a kai wa mayakan IS farmaki

Shugaba Hollande na Faransa da Masum na Iraki Hakkin mallakar hoto na
Image caption Shugaba Hollande na Faransa, Fuad Masum na Iraki

Ministocin harkokin waje na wasu kasashen duniya Talatin sun sha alwashin taimaka wa kasar Iraki a yakin da take yi da 'yan kungiyar masu jihadi.

Ministcin dai na wani taro ne a birnin Paris na kasar Faransa da nufin tsara dabarun yaki da Kungiyar masu jihadin.

Shugaban Faransa, Francois Hollande ya bayyana kungiyar da cewar wata babbar barazana ce da ke bukatar hadin-kan kasan duniya wajen tunkararta.