Ba za mu goyi bayan Jonathan ba- Lamido

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gwamna Sule Lamido na cikin gwamnonin jam'iyyar PDP ta shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan

Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya ce shi da jama'arsa ba za su goyi bayan sake takarar shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan a 2015 ba, sai an cika musu alkawarin yakin neman zabe a shekara ta 2011.

Gwamna Sule Lamido ya ce kawo yanzu babu wani daga cikin muhimman alkawuran da shugaba Jonathan ya daukar wa al'ummomin jihar Jigawa, da aka cika.

Ya ce wasu daga cikin alkawuran da Jonathan ya dauka amma bai cika ba, sun hada da fadada madatsar ruwa ta garin Auyo, da kuma daukar nauyin gina filin jirgin sama a jihar tare da ayyukan takaita kwararowar hamada.

Kawo yanzu dai shugaban kasar, bai bayyana cewa zai sake tsayawa takara a zaben shekarar 2015 ba.