'Yadda na ji da na zama Sarkin Kano'

Image caption Mai Martaba, Sarki Sanusi na biyu a cikin fadarsa

Sarkin Kano, Mai Martaba Muhammadu Sanusi na biyu ya ce abin ba zai misaltu ba, ya iya bayyana yadda ya ji da aka nada shi Sarkin Kano.

A hirarsa da editan sashen Hausa na BBC Mansur Liman, Sarki Sanusi ya ce "Abu ne mai wuya mutum ya suranta yadda mutum ya ji a wannan lokacin. Na farko dai dukkan dan Sarki yana da burin Allah ya ba shi gadon gidansu."

Sarkin Kano din ya kara da cewar " Idan sarauta ta fadi, a lokacin wato wani hali ake shiga na kowa yana jira ya ji mai Allah zai yi. Na farko muna godiya ga Allah saboda shi ke nada wa. 'Ya'yan sarki na da yawa amma wanda Allah Ya zaba shi ne zai zama Sarki."

A kan batun yadda mulkin gidan sarauta yake, Sarki Sanusi ya ce "Daga safe har dare aiki ake yi a gidan sarauta saboda yawan mu'amala da mutane."

A cikin watan Yuni ne Sarkin Kano Mai Martaba Muhammadu Sanusi na biyu ya hau kan karagar mulkin Kano, bayan rasuwar Sarki Ado Bayero.

Hawan Sarki Muhammad Sanusi na biyu kan karagar mulkin Kano ya janyo kace-nace, kafin daga bisani kura ta lafa, har ya samu shiga fada, mako guda bayan nada shi.