Hama Amadou ya ce ana yi masa bi-ta-da-kulli

Kakakin Majalisar Dokokin Nijar, Hama Amadou ya ce bi-ta-da-kulli ce hukumomin Nijar ke yi masa game da zargin safarar yara da ake yi masa.

A wata hira ta musanman da BBC, Hama Amadou ya ce zargin safarar yaran an kirkiro shi ne domin rage masa tasiri ne a fagen siyasar kasar.

Kakakin Majalisar, wanda yanzu yake gudun hijira a Faransa, ya ce ya fice daga Nijar ne don kauce wa 'muguwar niyyar' mahunkuntan kasar.

"Ikon kasar mu ya koma ikon kama karya," in ji Hama Amadou.

Kakakin ya kuma ce ya dauki lauyoyi, don kare matarsa da ke fuskantar shara'a a Nijar din yanzu haka a bisa zargin safarar Jarirai.

Ya kuma ce zai koma Nijar.

A watan jiya ne Shugaban Majalisar ya fice daga kasar bayan wani kwamitin Majalisar dokokin kasar ya cire masa rigar kariya, don ya fuskanci shara'a.