Scotland: Aski ya zo gaban goshi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Al'ummar Scotland na cikin tsaka mai wuya

An shiga rana ta karshe ta kamfe a Scotland, inda al'ummomin yankin a gobe alhamis za su yanke hukunci a kan ko su ci gaba da kasancewa karkashin Burtaniya ko kuma a'a.

Jagoran masu goyon bayan samun 'yancin cin gashin kan Scotland, Alex Salmond ya roki masu kada kuri'a kada su bari wannan dama ta samun kasa mai 'yancin cin gashin kai ta sullume.

Ya ce zaben raba gardamar muhimmiyar dama ce a gare su.

Kuri'un jin ra'ayoyin jama'a da aka gudanar a lokuta daban-daban har sau uku, sun nuna cewa tazarar da ke tsakanin masu neman ballewa da kuma masu son yankin ya ci gaba da zama karkashin Burtaniya ba ta da yawa sosai.