'Yan tawayen Ukraine na nazarin doka

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Matakin na daga cikin yunkurin karfafa yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma

Wani jagoran 'yan tawaye a gabashin Ukraine ya shaida wa BBC cewa sabuwar dokar da ke ba su ikon cin gashin kan yankunan da ke hannunsu, ba za ta hana su samun 'yancin kai ba.

Sai dai Andrei Purgin wanda ya fito daga yankin Donetsk ya ce dokar ta kunshi wasu abubuwa masu kyau da za su kasance ginshiki wajen sasantawa.

Ya ce a halin yanzu suna nazari a kan dokar, don kuwa akwai wasu abubuwa masu kyau da za su iya amfani da su wajen sassantawa amma hakan ba yana nufin sun karkata daga kan alkiblar da suka dosa ba ne.

Kudirin dokar wadda Majalisar dokokin Ukraine ta amince da shi, ya yi afuwa ga wasu 'yan tawaye, ko da yake, ban da wadanda suka aikata miyagun laifuffuka.

Wannan na daga cikin yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma don kawo karshen rikicin da ya shafe watanni biyar a yankin.