Boko Haram: Ana bukatar tallafin $34 miliyan

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mata da kananan yara na cikin mummunan yanayi a jihohin Borno da Adamawa

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, UNHCR ta yi kiran a samar da dala miliyan 34 domin tallafa wa dubban mutane da suka tsallaka kasashe makwabta daga Nigeria, sakamakon rikicin Boko Haram a jihohin arewa maso gabashin kasar.

Hukumar ta ce mutane fiye da 75,000 ne suka tsallaka zuwa kasashen Kamaru, da Chadi, da kuma Nijar daga bara zuwa yanzu.

Hukumar ta ce, sakamakon aika-aikar 'yan Boko Haram a jihohin Adamawa da Borno da kuma Yobe a yanzu haka dubun dubatar mutane na bukatar taikamako domin a ceci rayuwarsu.

Hukumar ta UNHCR tare da wasu kungiyoyi 16 da ke aikin gaji sun ce, a cikin watan Agusta kadai mutane fiye da 11,000 sun tsallaka zuwa Kamaru da Chadi a yayinda wasu fiye da 15,000 suka tsallaka yankin Diffa na Nijar.

Hukumar ta ce, saboda yadda 'yan Boko haram suka tsannanta kai hare-hare a cikin watan Satumba, a yanzu haka dubban mutane suna ta rasa muhallansu kuma watakila, daga nan zuwa karshen shekara, adadin 'yan gudun hijira ya haura mutane 95,000.