Mutane 18 ne suka mutu a harin FCE Kano

Image caption Cikin wadanda suka mutu har da mace mai ciki

Hukumomi sun ce kimanin mutane 18 ne suka ce sun hallaka, yayin da sama da 30 suka samu raunuka a harin da wasu 'yan bindiga suka kai a Kwalejin Ilimi ta Tarayya dake birnin Kano.

An dai kai harin ne a daidai lokacin da daliban makarantar ke tsakiyar daukar darasi a ranar Laraba.

Harin na daga cikin wadanda suka fi muni da aka taba kai wa a jihar ta Kano tun bayan kaddamar da hare-hare a jihar a farkon shekarar 2012.

A nasa bangaren Shugaban Nigeria ya jajantawa wadanda lamarin ya rutsa da su.

Rahotanni sun ce, 'yan bindigar sun saka abubuwan fashewa, sannan suka yi ta harbin kan-mai-uwa-da-wabi.

Kawo yanzu ba a san wadanda ke da alhakin kai wannan harin, sai dai a baya kungiyar Boko Haram ta kai hare-hare a jihar wadanda suka janyo asarar rayukan daruruwan jama'a.