ISIS : An kama mutane 15 a Australia

Jamian 'yan sanda Australia Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jamian 'yan sanda Australia

'Yan sanda a kasar Australia sun sanar da cafke akalla mutane 15 da ake kyautata zaton suna shirin aiwatar da wasu ayyukan ta'addanci.

Bayanai na nuna cewa mutanen wadanda aka alakanta da kungiyar ISIS mai fafutukar kafa daular musulunci, na shirin gille 'kan mutane.

Wakilin BBC ya ce kamen , na zuwa ne a dai dai lokacin da hukumomin Australian suka kara tsaurara matakan yaki da ayyukan ta'addanci.

Jamian 'yan sanda sun ce za'a gurfanar da wani mutum gaban kotu a yau dinannan game da zargin aikata miyagun laifuka masu alaka da ta'adanci.