An kashe mutane hudu a Kamba

Jamian yan sanda Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jamian Yan sanda a Najeriya

Rundunar 'yan sanda Najeriya ta ce mutane hudu ne suka hallaka a garin Kamba dake Jihar Kebbi bayan wani yamutsi da aka samu tsakanin mazauna garin da kuma jami'an 'yan sanda.

Lamarin ya faru ne bayan da aka kama wani mutun da ake zarginsa da satar mutane abin da ya sa mazauna garin suka nemi 'yan sanda su mika masu mutumin amma 'yan sandan suka nuna tirjiya.

A cikin wata sanarwar da kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya Emmanuel Ojukwu ya aikewa BBC ya ce an kafa dokar hana fita a cikin garin.

Ya kuma bayana cewa an kona motocin 'yan sanda biyu da babura tara a caj ofis din 'yansanda kuma an kona gidan DPO.

Ya kuma ce an kama mutane 89 da ake zargin suna da hanu a cikin lamarin.

Shi ma Spetan janar na 'yan sanda, Suleiman Abba ya nemi jama'a akan su daina daukar doka da hanunsu, a cewarsa kamata ya yi su rika taimakawa jami'an 'yansanda wajen tabbatar da doka da oda a cikin alumma.