2015: Gwamnonin PDP sun ce sai Jonathan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Akwai rarrabuwar kawuna tsakanin 'yan Nigeria kan takarar Mr Jonathan a 2015

Wasu gwamnonin Nigeria da aka zaba a karkashin inuwar jam'iyyar PDP sun amince Shugaba Goodluck Jonathan ya kasance dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ba tare da hammaya ba a zaben 2015.

Gwamnan Akwa Ibom, Godswill Akpabio shi ne ya sanar da matsayin gwamnonin bayan kamalla taron da suka yi a ranar Laraba.

Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido a wata hira da BBC ya ce shi da jama'arsa ba za su goyi bayan takarar shugaba Goodluck a 2015 ba, sai ya cika alkawarin baya.

Kawo yanzu Mr Jonathan bai bayyana ba a fili ko zai sake tsayawa takarar shugaban kasa ko kuma a'a.

Haka kuma a yayinda kwamitin zartarwa na PDP ke shirin yin wani taro a ranar Alhamis, ana saran jam'iyyar za ta amince da ranar 6 ga watan Disamba a matsayin ranar da za a yi taron zaben fitar da gwani na dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar.

Sannan kuma ana saran gudanar da zaben fitar da gwani na gwamnonin PDP a ranar 29 ga watan Nuwamba sai kuma na 'yan majalisar wakilai da kuma dattijai a ranar 22 ga watan Nuwambar, 2014.