An kaddamar da sabuwar wayar Blackberry

Hakkin mallakar hoto blackberry
Image caption Ana sa rai Blackberry Passport ta daga kasuwar wayoyin kamfanin

Kamfanin Blackberry ya kaddamar da wayar salula da ta banbanta da saura, wadda ke da fadin fuska da kuma madannan shigar da harufa na zahiri.

Ana iya sarrafa wayar mai suna Blackberry Passport, ta hanyar taba fuskarta da hannu, ko kuma yin amfani da madannan shigar da harufa na zahiri.

Cinikin wayoyin Blackberry dai ya na cigaba da yin kasa a dan tsakanin nan.

Masharhanta sun ce akwai yiwuwar sabuwar wayar Blackberrin ta sa ke jan ra'ayin masu amfani da wayoyin kamfanin, da kuma masu amfani da wayoyin salula da ba na Blackberry ba.

Wani babban jami'in kamfanin, Marty Beard ya ce kaddamar da sabuwar wayar Blackberrin, wani bangare ne na dabarun farfado da kasuwar wayoyin Blackberry da shugaban kamfanin John Chen ya bullo da su.

''Kwanan nan za a ga mun kara azama'' inji Mr. Beard.

Mr. Beard ya ce fadin fuskar wayar zai ba masu amfani da ita damar ganin ko ina na wasu shafuffuka sabanin yadda wasu wayoyin suke nuna wa.

Hakkin mallakar hoto blackberry
Image caption Wayar Blackberry Passport ta na daukan manhajojin BB da na Android

Kamfanin ya sanya wa wayar suna Passport ne saboda fadin fuskarta ya yi kama da Fasfo na tafiye tafiye.

Fadin fuskar wayar ya kai inci hudu da rabi, kuma tana da karfin nuna hoto (453 pixels), wanda ya fi na wayar iPhone 6 Plus ta kamfanin Apple, amma bai kai na Samsung Galaxy Note 4 ba.

Anyi madannan shigar da harufa na zahiri na wayar yadda ko kadan aka taba su, su nuna. Hakan ya bada damar kirkirar gajeren zango na sarrafa wasu manhajojin wayar cikin sauki, abinda sauran wayoyin Blackberry ba sa yi.

A yanzu ana sayar da Blackberry Passport ne akan farashin fara shigarta kasuwa, dala 599, kuma wayar tana daukan manhajojin Blackberry da na Android.

Cinikin wayoyin Blackberry dai ya yi kasa a 2014, inda bayanan da kamfanin ya fitar suka nuna wayoyi miliyan daya da dubu dari shida aka sayar a watanni uku zuwa Yuni.

Hakan babban ja baya ne idan aka kwatanta da da wayoyi miliyan shida da dubu dari takwas da kamfanin ya sayar a irin wannan lokaci a 2013, da kuma wayoyi miliyan goma sha uku da dubu dari biyu a 2011.