IS: Burtaniya za ta kara daukan mataki

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mr. Cameron ya bukaci kasashen duniya su hada hannu a yaki ta'addanci

Firaiministan Burtaniya, David Cameron ya ce yakamata Burtaniya ta dauki sabon mataki na kare jama'ar kasar daga hadarin kungiyar da'awar kafa daular musulunci-IS.

Mr. Cameron lokacin da ya ke magana a wurin taron majalisar dinkin duniya a Amurka, ya ce ya na neman majaliasr Burtaniya ta yi zama ranar Juma'a domin neman amincewarta na sa hannun kasar cikin farmakin da ake kai wa kungiyar IS a Iraki.

Ya ce Burtaniya zata kara azama don kare jama'arta daga hadarin kungiyar IS, ganin yadda akalla mutane masu zafarfar akida 500 daga Burtaniyan su ka tafi Syria da Iraki don shiga cikin kungiyar.

Mahalarta taron sun amince da wani kuduri na kawo karshen kwararar masu jihadi daga kasashen duniya zuwa Iraki da Syria.

Shugaban Amurka Barack Obama ya ce ya yakar zafaffar akida ta musulunci, ba abune da za ayi kawai da matakin soji ba.