Ebola: Taswirar yaduwar cutar

Ebola

Cutar Ebola da ta barke a yammacin Afrika ta fito fili ne a watan Maris, kuma ta gawurta ta kasance mafi kisa tun lokacin da cutar ta fara bulla a shekarar 1976.

Cutar da ta bulla a wannan karon ita ce mafi muni a tarihi, domin ta kashe adadin da suka zarta dukkan mutanen da ta taba kashewa a baya jimlatan.

I zuwa 20 ga watan Satumba, cutar ta kashe mutane 2,811 a kasashe hudu; Laberiya da Guinea da Saliyo da Nigeria.

Mutanan da suka kamu da ita kuma sun zarta 5,800.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta tabbatar da cewa wannan adadin hasashe ne, bai kai hakikanin adadin mutanen da cutar ta shafa ba, domin za a iya samun kusan mutane 20,000 da cutar ta kama nan da watan Nuwamba mai zuwa idan ba a dada inganta daukar matakan magance cutar ba.

Wuraren da Cutar ta barke a yanzu

Hakkin mallakar hoto BBC Hausa

Wuraren da cutar ta barke a baya

Hakkin mallakar hoto BBC Hausa

Karin bayani