Facebook: Amfani da jirgi mara matuki

Facebook Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Amfani da jirgi mara matuki zai karfafa ayyukan sadarwarmu

Kamfanin Facebook na duba yuwuwar yin amfani da jirgi mara matuki domin kyautata ayyukansa.

A cewar kamfanin hakan zai taimaka wajen samar da intanet ga kashi biyu cikin kashi ukun al'umar duniya, wadanda ba sa samun yin damar sada zumunta.

Akalla guraban ayyuka miliyan 140 ake sa ran hakan zai bayar da damar samarwa.

Kamfanin ya kara da cewa hakan zai magance matsalar talauci ga mutane miliyan 160, zai kuma rage yawan mace macen yara kanana.

Darekten dake kula da sashin ayyukan kere-kere a kamfanin na Facebook, Yael Maguire ne ya bayyana haka a wani taro da aka yi a Birnin New York.

"Jirgin zai kai kusan girman babban jirgin daukar fasinja na 747, a wasu lokuta ma zai tsaya a sararin samaniya na tsawon watanni ko ma shekaru." in ji Maguire.

Sai dai ya ce jirgin ba zai kasance mai nauyi ba, kuma nan da shekara mai zuwa ake san ran za a fara gwaji a kasar Amurka.

Ko da ya ke bayanai na nuna cewa yadde ake samar da jirage marasa matuka ido a duniya zai iya kawo cikas wajen hanzarin da ake yi na samar da wannan ci gaba.