Malamai sun yi tir da 'daular musulunci'

Hakkin mallakar hoto other
Image caption Kungiyar IS na ikirarin kafa 'daular musulunci'

An bukaci Malamai da jagororin addinin musulunci a fadin duniya su sanya hannu kan wata budaddiyar wasika da ke yin tir da ayyukan kungiyar daular musulunci.

Rahotanni sun ce malaman addinin musulunci fiye da 100, sun sanya hannu a kan wasikar, wacce ta yi watsi da akidar kungiyar.

Wani malami, kuma shugaban majalisar nazarin ilmin Fiqhu a Amurka ta arewa, Dakta Muzammil Siddiqi ya ce haramun ne fille kan 'yan jaridun kasashen yamma, don kuwa ba musulunci ba ne kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

A wani taron manema labarai a birnin Washington, shugabannin musulmin wadanda suka fitar da wasikar sun bukaci mutane su daina kiran kungiyar da Daular musulunci, don kuwa hakan na ingiza ta ne a kan akidar farfado da daular khalifanci.