Mace-macen yara kanana a nahiyar Afrika

A watan Satumbar shekarar 2000, shugabannin kasashen duniya suka amince da wasu kudurori guda takwas da ake yiwa lakabi da Muradun Karni ko MDGs a turance. Kudurorin na kunshe da abubuwan da za su inganta rayuwar yara a duk fadin duniya, a fannonin da suka hadar da lafiya, da ilmi, da sauransu.

Muhimmi a cikin kudurorin shi ne rage adadin yara da ke rasa rayukansu kafin su cika shekaru biyar a kasashe masu tasowa. Mahimbo Mdoe, na hukumar kula da yara ta Majalisar Dinkin Duniya Unicef, ya bayyana cewa kasar Malawi ta samu nasara sosai wajen cimma wannan muradin.

An samu ci gaba, sai da har yanzu yara na mutuwa

An samu gagarumin ci gaba wajen rage mace-macen yara a duniya, sai dai duk da haka fiye da yara miliyan shida ne ke rasa rayukansu a kowacce shekara kafin su cika shekaru biyar, kuma yawancinsu suna rasa rayukansu ne sakamakon cututtukan da za a iya maganinsu.

Kuma kasashen Afrika kudu da sahara sun fi samun mace-macen yara a duniya. Idan aka yi amfani da kididdigar shekarun 1990, kudurin Majalisar Dinikin Duniya shi ne rage mace-mace da kashi biyu cikin uku zuwa karshen shekarar 2015. Kasar Malawi na daga cikin kasashen Afrika kalilan da suka cimma wannan muradin.

Mace-Macen Jarirai

Makwanni hudun farko na rayuwar kowanne jariri sun fi hadari. Duk da cewa an samu raguwa a mace-macen jarirai, raguwar ba ta kai ta yara masu kananan shekaru ba. Don haka mace-macen jarirai na ci gaba da daukar kaso mai tsoka a cikin mace-macen yara 'yan kasa da shekaru biyar. A shekarar 2013, jarirai miliyan biyu da dubu dari takwas ne suka mutu kafin su cika kwanaki 28 a duniya.

Yaushe za a cimma muradun karni?

Tsakanin shekarun 1990 da 2013, yara miliyan 223 ne suka rasa rayukansu a duk fadin duniya kafin su cika shekaru biyar - kwatankwacin adadin al'ummar Brazil. A yanayin da ake ciki, ba za a iya cimma muradun Majalisar Dinkin Duniya na rage mace-macen yara kafin shekarar 2026 ba.

Me ke janyo mace-macen yara?

Yawan mace-macen jarirai a watan farko na haihuwar su ya kai kashi 44% na dukkan mace-macen jarirai 'yan kasa da shekaru biyar. Kusan kashi 60% na wadannan mace-macen na faruwa ne sakamakon matsalolin da ake samu a lokacin haihuwa.

Karin bayani