'Yan sanda sun tsinci 'yar Chibok a Mubi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan matan Chibok sun shafe fiye da kwanaki 160 a hannun 'yan Boko Haram

Rundunar 'yan sandan Nigeria ta ce an tsinci wata yarinya a Mubi da ake zaton tana daga cikin 'yan matan Chibok da kungiyar Boko haram ta sace.

Kakakin rundunar Emmanuel Ojukwu wanda ya tabbatarwa da BBC hakan ya ce 'yan sanda ne suka tsinci yarinyar mai kimanin shekaru 20 a daji da yammacin ranar Laraba'.

Majiyar 'yan sandan ta ce a halin yanzu ana kula da ita a wani asibiti da ke garin Yola, kuma ana yi mata tambayoyi.

Fiye da 'yan mata 'yan makaranta 200 ne dai ke ci gaba da kasancewa a hannun kungiyar tun bayan sace su da ta yi a watan Afrilun da ya gabata.