Ebola: An killace larduna 3 a Saliyo

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hukumar lafiya ta duniya ta ce mutane kusan 3,000 suka mutu

Saliyo ta killace karin wasu lardunan kasar uku don yaki da cutar Ebola.

Hakan na nufin an killace biyar daga cikin lardunan kasar 14, kimanin kashi daya cikin uku na al'ummar kasar.

Yunkurin ya biyo bayan matakin hana fita na kwana uku da ya kawo karshe ranar Lahadin da ta gabata.

Da yake jawabi da maraicen ranar laraba, Shugaban kasar, Ernest Bai Koroma ya ce killacewar za ta sanya al'umma cikin wahala, sai dai ya ce tserar da al'ummar kasar shi ne gaba da komai.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce mutane kusan dubu uku ne suka mutu sakamakon cutar Ebola a yankin Afirka ta yamma.