UNHCR ta kwashe 'yan gudun hijirar Nigeria 8,000

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rikicin Boko Haram ya tilastawa mutane da dama barin gidajensu

Hukumar kula da 'yan gudun Hijira ta Majalisar dinkin duniya UNHCR ta kwashe 'yan gudun hijirar Nigeria fiye da 8,000 daga wuraren da suke fakewa a Kamaru zuwa sansanin Minawao.

Dubun- dubatar 'yan gudun hijira ne suka tsallaka kan iyaka daga Nigeria zuwa Kamaru sakamakon hare-haren kungiyar Boko Haram.

'Yan gudun hijirar na rayuwa ne a garuruwa daban-daban wadanda suka yi iyaka da Nigeriar kamar Fotokol da Amchide da Mora da kuma Kolofata karkashin mawuyacin hali.

Har yanzu akwai dubban 'yan gudun hijirar Nigeria dake warwatse a yankin arewa mai nisa a Kamaru da suke jiran a kai musu agaji.