Cin zarafin mata a Afghanistan

Hakkin mallakar hoto AP

'Yan sanda a tsakiyar Afghanistan na neman wani mutum wanda ake zargin ya yanke wa matarsa wani bangare na hancinta da wukar dakin girki.

Shugabar sashen kula da harkokin mata a lardin Daykundi ta yi zargin cewa mutumin ya taba cutar da matar a baya inda ya cire mata farata, a wani lokaci kuma ya kulle ta har tsawon mako guda ba tare da abinci ko ruwan sha ba.

A shekarar da ta gabata hukumar kare hakkin dan adam ta kasar ta ce cin zarafin mata ya karu da kusan kashi 25% idan aka kwatanta da shekarar 2012