Google na fuskantar matsin lamba

Google Hakkin mallakar hoto AP
Image caption google ya ce ya na hada kai da hukumomi domin kare bayanan sirrin jama'a

Masu kula da bayanan sirri a nahiyar turai, suna ci gaba da nuna matsin lamba ga kamfanin Google kan sauya tsarin kare bayanai.

Wannan na faruwa ne shekaru biyu bayan da kamfanin na Google ya sauya tsare-tsarensa, wadanda suka sabawa dokar nahiyar.

Baya ga haka an kuma yi kira ga kamfanin da ya bayyanawa mutane irin bayanan da ya ke diba da kuma wadanda yake rabawa.

Kamfanin dai ya ce yana kan aiki da hukumomin dake tabbatar da cewa an kare bayanan sirri jama'a domin bayyana yadda tsare tsarensa suke kan wannan batu.

Wannan takaddama ta samo asali ne tun a watan Maris din shekarar 2012 bayan da Google ya tattara wasu tsare-tsarensa a wuri guda ya kuma fara hada bayanan da na Youtube, Gmail da taswirar Google.

Yanzu haka babu wata madafa dangane da hakan idan har mutane na son ficewa daga sauye-sauyen.

Ba a dai taba zargin Google kai tsaye kan saba doka ba sai a wannan batu na saba dokar hukumar ta tarayyar turai.

" Mun yin aiki da hukumomi daban daban dake kare bayanan sirrin jama'a a nahiyar turai da kuma yadda muke adana bayanan." In ji Kakakin kamfanin na Google.