'Yan Nigeria sun yi zanga-zanga a New York

Majalisar Dinkin Duniya
Image caption Majalisar Dinkin Duniya

Wata gamayyar kungiyoyin da ba na gwamnati ba daga sassan Nigeria ta gudanar da zanga-zanga don gabatar da korafe-korafenta ga Majalisar Dinkin Duniya a New York.

Kungiyoyin sun gabatar wa Majalisar korafe-korafe a kan yadda gwamnatin Nigeria ke tafiyar da harkokin kasar ta fannin tsaro da siyasa da sauran abubuwa da suka jibanci mulki.

Sun yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya don ta mayar da hankali a kan kasar saboda matsalar rashin tsaro da ke addabar yankin arewa maso gabashi.

Sun kuma ce za su nemi Majalisar ta shiga batun wani jirgin sama da aka kama a kasar Afrika da Kudu dauke da makudan kudade da aka yi nufin sayen makamai don kai wa Nigeria.