Samir Nasri zai tafi jinya

Samir Nasri Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Samir Nasri ba zai buga wasansu da Hull City ba

Dan wasan tsakiya na Manchester City Samir Nasri, zai kwashe wata guda yana jinya saboda rashin lafiya da yake fama da ita.

Za dai a yi ma dan wasan mai shekaru 27 tiyata ne a mararsa, kamar yadda hukumomin kungiyar suka tabbatar.

Ko a baya ma Nasri bai samu bugawa City wasanta na Capital Cup ba wanda ta samu nasarar doke Shieffield Wednesday da ci 7-1.

"Abin na shi ya tsananta, saboda haka ina ganin zai kwashe wata guda yana jinya." In ji kocin City Manuel Pellegrini yayin da yake bayyana cewa Nasri ba zai buga wasansu da Hull City a gasar Premier ba.