Ma'aikatan ilmi na yajin aiki a Nigeria

Image caption Yajin aiki tsakanin Ma'aikata musammam ma a bangaren ilmi abu ne da ya zama ruwan dare

Ma'aikata a Shalkwatar ilmi ta tarayyar Najeriya sun shiga wani yajin aiki saboda kin biyan wasu hakkokinsu.

Tun ranar litinin ne kungiyar manyan ma'aikatan gwamnati ta garkame Shalkwatar ilmi da ke sakatariyar gwamnatin tarayya da sauran ofisoshinta a fadin kasar.

Yajin aikin dai ya hana ministan ilmin Nigeria, Malam Ibrahim shekarau da sauran jami'ai shiga wuraren aikinsu.

Jami'in ya ce sun shiga yajin aikin ne kan batutuwan da suka hadar da rashin karin albashi ga ma'aikatan da aka yi wa karin girma daga mataki na 12 zuwa har mataki na 15 da rashin biyan kudaden alawus na masaukin da ma'aikatan suka yi amfani da shi bayan sun samu sauyin aiki.