Apple ya maida martani kan Iphone6

Kamfanin Apple ya maida martani kan zargin da wasu suka yi a kan cewa sabuwar wayar salularsa ta Ihone6 kan lankwashe sai dai ya ce abun ne mai wuya hakan ta kasance.

Kafofin yadda labarai a sassan duniya daban daban sun samar da rahotani da ke cewa masu amfani da wayar iphone 6 da dama sun yi korafin cewa wayar kan lakwashe idan an sakata cikin aljihun wando batare da tana cikin gidanta ba.

Abokan gogaya na kamfanin Apple suma sun yi ta yadda korafe korafen mutane.

Hakkin mallakar hoto APPLE

Kamfanin Apple dai ya ce mutane tara dake amfani da wayar ne suka fada masa cewa wayarsa ta iphone 6 kan lankwashe.

Lamarin ya sa hannayen jarin kamfanin Apple faduwa bayan masu amfani da wayoyinsa suka sa hotunan wayoyin da suka lankwashe a shafukan internet.

Haka kuma akwai rahotanin da ke cewa kamfanin ya cire wata naura da ake kira ios 8 bayan korafin da masu amfanin da iphone 6 suka yi akan cewa basa iya kira ko samun kira saboda naurar.

Sai dai wani mai sharhi ya ce Apple be ba ta lokaci ba wajen maida martani kan rahotanin da suka ce ko baya ma wayoyinsa sun lankwashe a shekarar 2010 lokacinda ya fitar da iphone 4 cikin kasuwa.

Hakkin mallakar hoto AP

Tuni kamfanonin wayoyin salula dake gogaya da Apple irinsu Samsung da LG da HTC suka walafa sakonin a shafinsu na twitter game da cece- kucen da ake yi kan wayoyin Apple.

Kamfanin LG a shafinsa na twitter ya yi amfani da kalmar bendgate da masu amfani da wayar Iphone din Apple suka yi akan zargin.

A baya bayanan ne kamfanin Apple ya yi shellar cewa ya sayar da wayoyin Iphone 6 da kuma Iphone6 plus guda miliyan goma.

Sai dai bayanai sun ce wayoyin Samsung da Sony da Blackberry da kuma sauransu su ma sun lankwashe a baya,