Majalisar Dokokin Birtaniya za ta kada kuri'a kan IS

Hakkin mallakar hoto PA

A yau majaliar dokokin kasar Birtaniya za ta kada kuri'a kan ko ya dace kasar ta shiga yakin da Amurka ta ke yi da kawayenta akan 'yan kungiyar IS mai fafatukar kafa daular musulunci a kasashen Iraqi da Syria.

A baya dai Majalisar ta ki amincewa daukan matakin sojin akan gwamnatin shugaba Bashr Al Assad na Syria.

Wannan na faruwa ne a dai dai lokcin da Firai ministan Australia, Tony Abbott, ya ce nan da kwanaki kadan masu zuwa, gwamnatinsa za ta yanke shawarar shiga yakin.

A cewar Firai ministan, Australia na da rawar da za ta taka a wannan yaki, ganin irin munanan ayyukan da kungiyar ke aikatawa.