Ana bukatar sojin kasa a Syria da Iraki

Janar Martin Dempsey Hakkin mallakar hoto
Image caption Janar Martin Dempsey

Babban Hafsan sojin kasar Amurka, Janar Martin Dempsey, ya ce hare haren da aka kaiwa kungiyar IS mai da'awar kafa daular musulunci a Syria da Iraqi, sun kassara ayyukan kungiyar.

Sai dai ya yi gargadin cewa, hare hare na sama, ba su isa a ce sun samar da galabar da ake bukata akan kungiyar ba, inda ya kara da cewa yin amfani da dakarun kasa zai yi tasiri matuka a yakin da ake yi da kungiyar.

A farkon makon da muke ciki janar Demosey ya bayana gaban wani kwamiti na Majalisar datawan Amurka inda ya ce a wani mataki na fadan me yuwa a tura da sojojin kasa sai dai ya ce ba dole bane sojojin su kasance daga Amurka

Janar Dempsey ya kuma kara da cewa a ganinsa sojojin da zasu iya wannan aiki sune hadakar sojojin Iraki da na Kurdawa da kuna yan tawaye masu sassaucin ra'ayi da ke adawa da gwamnatin Syria.

Haka kuma Janar Dempsey ya ce a Syria kadai za'a bukaci sojoji kusan dubu goma sha biyu zuwa dubu goma sha biyar .

Tuni Majalisar Dokokin Amurka ta amince da shirin samar da horo da kuma makamai ga yan tawaye masu sassauncin ra'ayi kusan dubu biyar .