FBI ta damu da matakan kare bayanai

FBI Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Comey ya ce kare bayanan sirri a wayoyi zai kawo cikas ga jami'an tsaro

Hukumar bincike ta FBI a Amurka, ta ce shirin da kamfanonin Google da Apple ke kokarin aiwatarwa na kare bayanan sirri babban abun damuwa ne.

Yayin da yake ganawa da manema labarai, shugaban hukumar ta FBI, James Comey, ya ce shirin zai iya kawo cikas ga ayyukan bincike da hukumomin tsaro ke gudanarwa.

Ya kara da cewa, rayuwar mutane da dama, ta dogara ne akan yadda hukumar ke samun bayanan sirri da masu aikata manyan laifuka ke amfani da su.

Yanzu haka Google na fuskantar matsin lamba daga kungiyoyin nahiyar turai dake sa ido kan ganin an kare bayanan sirrin jama'a, inda aka yi kira ga kamfanin ya tsaurara matakan kare bayanan jama'a.

To sai dai hukumar ta FBI, ta ce samar da wani tsari na kare bayanai zai zama babban kalubale ga ayyukansu.

"Bana kauna inga mutane suna tambaya ta yadda muka kasa kare rayuwar wani yaro, ko kuma dalilin da ya sa ba mu dauki wani mataki." In ji Comey.

Kalaman Comey na zuwa ne tun bayan da kamfanin Apple ya bayyana wani shirinsa na samar da wata kafa da za ta kare satar bayanai a sabuwar wayar iOS 8 wacce ba ta da mabudi.

Hakan kuma na nufin, Apple ba shi da hurumin baiwa 'yan sanda wasu bayanai dake kan wayar.